Kofin Duniya: Real Madrid ta kai wasan karshe

Cristiano Ronaldo na cin kwallo ta biyu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kwallon Ronaldo ita ce ta 500 da ya ci, tun lokacin da ya fara wasa a kungiya

Real Madrid ta kara bajintar yin wasa 36 ba tare da an doke ta ba, inda ta casa kungiyar Club America 2-0 ta kai wasan karshe na cin kofin duniya na kungiyoyi.

Karim Benzema ne ya fara ci wa Zakarun na Turai, Real Madrid, kwallo a daidai lokacin da za a tafi hutun rabin lokaci a wasan da ake yi a Japan, bayan da Toni Kroos ya tura ma sa kwallo.

Bayan an dawo wasa, ana dab da tashi ne a karin lokaci, sai Cristiano Ronaldo, ya kara ta biyu, amma kuma an samu rudani kan tabbacin shigar kwallon raga.

Daga nan ne sai alkalin wasa Enrique Caceres, ya bukaci bayanin mataimakinsa mai duba hoton bidiyon wasan, inda daga nan ne ya tabbatar da ta ci.

An dai fara amfani da tsarin mataimaki alkalin wasa mai duba hoton bidiyon a wasa a gasar ta bana, domin taimaka wa alkalin wasa warware duk takaddamar da ta taso wadda ba a iya gani ko tantance ta ba a lokacin wasan.

Yanzu Real Madrid za ta fafata a wasan karshe da Zakarun Asia, Kashima Antlers ta Japan, wadda ranar Laraba ta doke Atletico Nacional ta Colombia 3-0, a daya wasan na kusa da karshe.

Karim Benzema na cin kwallon farko

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Benzema ya zama dan wasan Real Madrid da ya ci kwallaye a gasar ta kofin duniya daban-daban guda biyu

Ita dai gasar ta cin kofin duniya na kwallon kafa na kungiyoyi, zakarun nahiyoyi shida ne suke fafatawa a cikinta.

Kafin a fara wasan na Real Madrid an yi tsit na minti daya a filin na Yokohama Stadium, domin jimamin wadanda suka mutu a hadarin jirgin sama na 28 ga watan Nuwamba, wanda ya hallaka mutum 71, da suka hada da 'yan wasa 19 da jami'ai na kungiyar Chapecoense ta Brazil.