Chelsea ta ci wasannin Premier 11 a jere

Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea ta bayar da tazarar maki tara

Chelsea ta ci gaba da zama a matsayi na daya a kan teburin Premier, bayan da ta doke Crystal Palace da ci 1-0 a fafatawar da suka yi a ranar Asabar.

Chelsea ta ci kwallon ne ta hannun Diego Costa, kuma na 13 da ya zura a raga jumulla a gasar Premier ta bana.

Kungiyar wadda Antonio Conte ke jagoranta ta ci wasannin Premier 14, inda ta yi canjaras a karawa daya, sannan aka doke ta a wasanni biyu.

Da kuma wannan sakamakon Chelsea ta ci wasanni a gasar Premier sau 11 a jere, wanda ta taba yin hakan a kakar wasa ta 2009 tsakanin watan Afirilu zuwa Satumba.

Chelsea tana nan a matakinta na daya a kan teburi da maki 43, za kuma ta buga wasan gaba ne da Bournemouth.