A ranar Juma'a NFF ta ce ta bai wa 'yan Super Falcons kudin da suke bin ta bashi

A ranar Juma'a NFF ta ce ta bai wa 'yan Super Falcons kudin da suke bin ta bashi

Hukumar ta NFF ta samu biyan bashin ne, bayan da gwamnatin Nigeria ta ba ta Dala Miliyan daya da dubu dari da saba'in domin ta biya ladan lashe kofi da hakkokin Super Falcons.

A ranar Larabar da ta gabata ne 'yan wasan na Super Falcons, wadanda suka lashe kofin kwallon kafar nahiyar Afirka na mata a watan Disamba a Kamaru, suka yi zanga-zanga zuwa Majalisar Dokoki da fadar Shugaban kasa saboda rashin biyansu kudaden da ya kamata a ba su.