Leipzig ta sake darewa kan teburin Bundesliga

Gasar Jamus

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A bara ne RB Leipzig ta samu damar shiga gasar ta Bundesliga

Kungiyar RB Leipzig ta sake komawa mataki na daya a kan teburin Bundesliga na Jamaus, bayan da ta ci Hertha Berlin 2-0 a ranar Asabar.

Timo Werner ne ya fara ci wa kungiyar kwallon kuma na tara da ya ci kenan a gasar ta Bundesliga ta bana, sannan mai tsaron baya, Naby Keita ya ci ta biyu.

Da wannan sakamakon, RB Leipzig, wadda ta shigo gasar Bundesliga a bara, ta bai wa Bayern Munich tazarar maki uku.

A ranar Lahadi ne Bayern Munich za ta ziyarci Darmstadt.