Man United ta doke West Brom da ci 2-0

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

United ta hada maki 30 a wasanni 17 da ta yi a gasar Premier ta bana

Manchester United ta doke West Brom da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na 17 da suka fafata a ranar Asabar.

United din ta ci kwallayenta biyu ne ta hannun Zlatan Ibrahimovic, wanda jumulla ya zura kwallaye 152 a raga a wasanni 170 da ya buga a bayan nan.

Da wannan sakamakon United ta hada maki 30, ita kuwa West Brom tana nan da makinta 23 bayan buga wasanni 17 a gasar ta Premier da suka yi.

Manchester United za ta buga wasanta na gaba da Sunderland, yayin da West Brom za ta kece raini ne da Arsenal.