Sakamakon wasannin damben gidan Ali Zuma

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Dambe takwas aka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria

Wasanni takwas aka dambata a gidan damben gargajiya na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria a ranar Lahadi da safe.

An fara da wasan da Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu ya buge Shagon Sojan Kyallu daga Arewa a Turmi na biyu.

Shi kuwa Shagon Buzu daga Arewa buge Shagon Bahagon Mai Maciji daga Kudu ya yi a turmin farko.

Shagon Isuhu Na Shandam daga Kudu a turmin na buyi ya doke Shagon Surajo daga Arewa.

Shi kuwa Dan Madobiya Kamasu Doguwa daga Arewa a turmi na uku ya sa Bahagon Dan Kanawa daga Kudu ya dafa kasa.

Sai wasannin da aka yi canjaras da suka hada da karawa tsakanin Shagon Bahagon Sisco daga Kudu da Shagon Habu Daba daga Arewa.

Da fafatawa tsakanin Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Shagon Shagon 'Yar Tasa da Arewa da na Shagon Buzu daga Arewa da Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu.

Wasan karshe da aka yi tsakanin Fatalwar Shagon Alabo daga Kudu da Shagon Dan Inda daga Arewa turmi uku suka yi babu wanda ya fadi a tsakaninsu.