Real Madrid ta lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi

Fifa World Club Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan ne karo na biyu da Madrid ta lashe kofin

Real Madrid ta ci kofin duniya na zakarun nahiyoyi, bayan da ta doke Kashima Antlers da ci 4-2 a fafatawar da suka yi a ranar Lahadi.

Real Madrid ta ci kwallon farko ta hannun Kareem Benzema a minti na tara da fara tamaula, sannan Cristiano Ronaldo ya kara ta biyu a bugun fenariti a minti na 60 ana murza-leda.

Ita kuwa Kashima Antlers ta fara cin kwallo ne ta hannun Gaku Shibasaki daf da za a je hutun rabin lokaci, kuma bayan da aka dawo ne daga hutun ya kara cin ta biyu.

Haka aka tashi wasa 2-2 daga nan ne ka yi karin lokaci na minti 30, wasan farko minti 15 ya sake fafatawa karo na biyu minti 15.

Nan ne fa Real Madrid ta samu damar kara cin kwallaye biyu ta hannun Cristiano Ronaldo, wanda hakan ya sa ta lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi.

Wannan ne karo na biyu da Madrid ta ci kofin bayan wanda ta dauka a 2014.

Matsayi na uku:

Kungiyar Atletico Nacional ta zama ta uku a gasar ta kofin zakarun nahiyoyi bayan da ta doke Club America a bugun fanareti 4-3.

Kungiyar Atletico Nacional ta Colombia ce ta fara cin kwallaye biyu, kafin Club America ta Mexico ta rama daya kafin hutun rabin lokaci.

Bayan an dawo ne Club America ta rama, har kuma aka kammala lokacin ka'ida a 2-2, sannan aka yi bugun fanareti.