An rage hukuncin hana Madrid sayen 'yan wasa

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi na bana karo na biyu
Kotun daukaka kararrakin wasanni ta duniya ta rage hukuncin hana Real Madrid sayen 'yan wasan tamaula zuwa kakar wasa daya.
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ce ta yankewa Madrid hukuncin hana ta sayo 'yan wasan kwallon kafa zuwa kakar wasanni biyu, bayan da aka same ta da laifin karya ka'ida.
Sai dai kuma hukuncin na nufin Madrid ba za ta sayi 'yan wasa ba a watan Janairun nan a lokacin da za a bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo har sai karshen kakar bana.
Haka kuma kotun ta rage tarar da aka ci Real Madrid daga dala 282,000 ya koma dala 188,000.
An dai samu Real Madrid da Atletico Madrid da laifin karya ka'idar sayen 'yan wasan kwallon kafa matasa masu kasa da shekara 18 a cikin watan Janairu.
Hukuncin bai yi jawabi kan daukaka karar da Atletico ta shigar da kuma tarar da aka ci ta ba.