Man United da Man City za su gwabza a Amurka

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyoyin biyu da ke garin Manchester masu buga gasar Premier za su ziyarci Amurka a shirin atisayen tunkarar kakar wasanni ta 2017.

Wasan hamayya tsakanin Manchester United da Manchester City a karon farko za su kece raini a Amurka idan an kammala kakar wasannin bana.

A watan Yuli da ya gabata Kociyan Manchester United, Jose Mourinho da na Manchester City, Pep Guardiola ya kamata su kara a Beijing.

Amma saukar ruwa kamar da bakin kwarya sa'o'i shida kafin a fara karawar ya sa aka dage fafatawar da aka tsara a baya.

Kungiyoyin biyu da ke garin Manchester masu buga gasar Premier za su ziyarci Amurka a shirin atisayen tunkarar kakar wasanni ta 2017.

Ba a bayar da karin bayani kan wasan ba, illa dai za su kece raini a gasar kofin International Champions Cup.