Premier: Southampton ta doke Bournemouth 3-1

Rodriguez na murnar kwallon da ya ci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rodriguez ya ci wa Southampton kwallaye hudu a bana, amma a bara uku ya ci

Southampton ta doke abokiyar hamayyarta Bournemouth da ci 2-1 a wasan Premier na mako na 17.

Aké ne ya fara jefa kwallo a ragar bakin, 'yan Southampton minti shida da shiga fili, kafin Bertrand ya rama a minti na14.

Sai kuma Rodriguez wanda a minti na 48 da na 85 ya ci kwallayensa na farko tun watan Agusta a gasar Premier, wadanda suka ba kungiyarsa nasara a wasan.

Yanzu Southampton ta zama ta bakwai a tebur da maki 24, yayin da Bournemouth ta ci gaba da zama ta 10 da maki 21.