Morinho: Ni na sa a ba wa magoya baya riguna

Wata mai goyon bayan Manchester United da ta dace da rigar Pogba.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Mourinho ya ce: Na ce su ba su rigunan ne domin lokaci ne na Kirsimeti.

Kocin Manchester United manager Jose Mourinho ya ce shi ya umarci 'yan wasansa su ba wa magoya bayansu rigunansu bayan nasarar da suka yi a kan West Brom 2-0 ranar Asabar.

Kyaftin Wayne Rooney da Paul Pogba da kuma Marcus Rashford dukkaninsu sun cire rigunansu suka kai wa magoya bayan nasu wadanda suka bi su domin kallon wasan, lokacin da aka busa tashi.

Mourinho ya kara da cewa : "Ba wa dan dan kallo riga ana gama wasa, wadda take da gumi abu ne mai muhimmancin gaske.

Abin takaici ni ba kowa ba ne zai samu rigar, amma wadanda suka dace suka samu, ba karmin jin dadi ba ne.''

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Magoya baya sun rukunkume Marcus Rashford lokacin da ya je bayar da rigarsa

Kwallo biyun da Zalatan Ibrahimovic ya ci wa United a wasan ya kasance 11 ya ci wa kungiyar a Premier, inda a tarihi Ruud van Nistelrooy dan Holland shi ne ya ci musu 12 a wasansa 16 na farko a gasar.

Manchester ta yi wasa 10 kenan ba tare da an doke ta ba aduk wasannin da take yi, kuma za ta yi wasanta na gaba da Sunderland ranar 26 ga watan Disamba.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Rooney na daya daga cikin 'yan wasan da suka ba wa magoya baya rigarsu