Man City ta doke Arsenal 2-1

Leroy Sane ya zura kwallo a ragar Arsenal

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Leroy Sane ya rama wa Man City minti biyu da dawowa daga hutun rabin lokaci

Manchester City ta doke Arsenal 2-1 a Etihad a wasansu na mako na 17 ranar Lahadi, abin da ya sa City ta zama ta biyu a tebur da maki 36, a bayan Chelsea mai 43.

Arsenal wadda ta fara cin kwallo a minti biyar kacal da shiga fili ta hannun Walcott, yanzu ta dawo ta hudu a tebur da maki 34.

Minti biyu da dawowa daga hutun rabin lokaci ne sai Leroy Sané ya rama wa Manchester City, kafin kuma a minti na 71 Raheem Sterling ya ci ta biyu.

Sai dai kuma zaman Mancester Cityn a matsayi na biyu zai iya zama na wucin-gadi kafin ranar Litinin, inda Liverpool za ta iya kawar da ita, idan ta yi nasara a gidan Everton.

Yanzu Arsenal ta maye gurbin Manchester City na da, matsayi na hudu a tebur.

Tarihin da aka kafa a wasan

Wanna ita ce nasara ta 16 da Guardiola ya yi a Man City

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wannan shi ne karon farko da Manchester City ta farfado ta yi nasara a wasanPremier da ake gabanta har aka tafi hutun rabion lokaci tun watan Nuwamba na 2012, wancan lokacin da Tottenham.

Ita kuwa Arsenal da wannan ta sha kashi sau uku kenan tana matsayi na 'yan gaba-gaba a wannan kaka, fiye da yadda suka yi a kakar da ta wuce, ind a wancan lokacin sau biyu kawai aka ci su, sun irin wannan matsayi

Haka kuma Gunners din su sha kashi wasannin Premier a jere, sun jagora a karon farko a tebur tun watan janairu na 2012, a wasansu da Fulham da Swansea a lokacin.

Har yanzu Guardiola bai yi rashin nanasara ba a gida a hannun Arsene Wenger a duk wata gasa.

Sane ya kasance dan wasan Jamus na shida da ya ciwa Manchester City kwallo a gasar Premier- abin da ya zarta na duk wata kungiya a gasar.

Tun da ya je Arsenal, Sanchez ya taka rawa a kwallaye 59 na Premier da kungiyar ta ci , shi da kansa ya ci 41, sannan ya bayar aka ci 18.

Sergio Aguero ne kawai ya fi shi wanda shi kuma yake da 60 da ya jefa raga da kansa ya kuma taimaka aka ci 10

.Shi kuwa dan wasan Manchester City Raheem Sterling kwallonsa ta farko ya ci ta premier a wasanni tara, tun lokacin da ya ci Swansea a watan Satumba.

Golan Arsenal Cech ya kafa tarihi a karon farko na yin wasan Premier takwas ba tare da an daga ragarsa ba .

Yanzu kungiyoyin za su yi wasansu na gaba a washegarin ranar Kirsimeti, inda Arsenal ke gida da West Bromyayin da Manchester City za ta je gidan Hull City.

Wasan Tottenham da Burnley

A daya wasan na ranar Lahadi Tottenham ta yi nasara a kan Burnley da ci 2-1, inda Spurs din ta ke ta biyar a tebur da maki 33, maki daya tsakaninta da Arsenal.

Burnley wadda ta fara cin kwallo a wasan ta hannun Barnes a minti na 21 tana matsayi na 16 da maki 17.

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Danny Rose ya ci wa Tottenham kwallonsa ta biyu ta Premier ta bana

Dele Alli ne ya farke wa Tottenham kwallonta a minti na 27 sannan kuma Danny Rose ya kara ta biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 71.