Leicester na son dawo da Joe Hart Ingila

Joe Hart

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Joe Hart na zaman aro a Torino ta Italiya daga Manchester City

Leicester City tana son sayen mai tsaron ragar Ingila da Manchester City Joe Hart, mai shekara 29 wanda ya tafi kungiyar Torino ta Italiya aro in ji jaridar Sun ta ranar Lahadi.

Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 35, na shirin yin watsi da goron gayyata na fan miliyan 120 daga wata kungiya ta China domin ya koma can da wasa.

A maimakon haka Ibrahimovic ya kwammace ya ci gaba da taka leda a Old Trafford har zuwa shekarar ta 2018, Kamar yadda jaridar Mail ta Lahadi ta ruwaito.

Tsohon kocin Ingila Sam Allardyce yana son dawowa aikinsa na koci a shekara mai kamawa 2017, in ji jaridar Sunday People.

Shi kuwa kocin Manchester City Pep Guardiola yana shirin taya dan wasan Arsenal ne Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 23 a kan fan miliyan 25 kamar yadda jaridar Sun ta Lahadi ta ruwaito.

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil, mai shekara 28, yana fadi-tashin ganin kungiyarsa ta sayo abokin wasansa na tawagar Jamus, Julian Draxler, mai shekara 23, daga Wolfsburg in ji RMC Sport.

Haka kuma Arsenal din na shirin saba ka'idarta ta biyan albashin fan dubu 200, a mako domin rike Alexis Sanchez, mai shekara 27, a wata yarjejeniya da ta kai fan miliyan 10 a shekara kamar yadda Mail ta Lahadi ta labarto.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Chelsea na harin dauko dan wasan gaba na Real Madrid Yames Rodriguez, mai shekara 25, a wani ciniki da ya kai fan miliyan 75, domin maye gurbin Oscar, mai shekara 25.

Dan wasan na Brazil tuni aka ruwaito cewa ya yi sallama da abokan wasansa a Chelsea, domin tafiya wasa, in ji jaridar Mirror ta Lahadi.

A bisa Yarjejeniyar da Wayne Rooney mai shekara 31 ya sabunta da kungiyarsa Manchester United, kyaftin din ba shi da damar tafiya wata kungiya da ke Ingila, in ji wani eja dan Italiya in ji Liverpool Echo.

Dan wasan tsakiya Philipe Coutinho, mai shekara 24, ga alama zai dawo fili a wasan da Liverpool za ta yi da Manchester City ranar jajiberin sabuwar shekaran nan ta 2017 kamar yadda tashar Sky Sports ta ruwaito kocin kungiyar Jurgen Klopp na cewa.

Manchester United ta taya dan wasan baya na Benfica Victor Lindelof mai shekara 22, a kan fan miliyan 38, kuma tana son ganin ta kawo shi OldTrafford a watan Janairu in ji jaridar Mirror ta Lahadi.

Wadannan labarai ne da wasu jaridun Burtaniya da kafofin watsa labarai na Turai suka ruwaito a ranar Lahadi.