Bonucci ya kawo karshen rade-radin komawarsa Chelsea

Leonardo Bonucci ya ci gaba da zama a Juventus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Leonardo Bonucci ya kuma yi wa Italiya wasa har sau 67

Dan wasan baya na Juventus Leonardo Bonucci ya sanya hannu a yarjejeniyar tsawaita zamansa a kungiyar har zuwa shekara ta 2021.

Kafin yanzu an bayar da rahotannin cewa dan wasan na Italiya zai koma Chelsea domin ya sake haduwa da tsohon kocin Juventus Antonio Conte a Chelsea.

Dan wasan mai shekara 29 ya koma zakarun na gasar Serie A, daga kungiyar Bari a shekara ta 2010, kuma tun lokacin ya yi wa zakarun wasanni 291.

A tsawon wannan lokaci ya dauki kofi biyar a jere na lig din Italiya da kofin kalubale na kasar guda biyu.

Sannan kuma sun kai wasan karshe na kofin zakarun Turai na 2015.