Ingila ta bullo da shirin samar da koci-koci 'yan kasar

Paul Scholes na cikin samun horon zama koci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Paul Scholes yana samun horon zama koci a Blackburn Rovers

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bullo da wani shirin taimaka wa tsoffin 'yan wasan kasar su shiga aikin horad da 'yan wasa domin kare su daga ficewa daga harkokin wasan.

Tuni tsohon dan wasan Manchester United Paul Scholes na cikin wani shiri na kpoyin aikin horarwar.

Kuma hukumar ta FA tuni ta tuntubi tsohon kyaftin din Liverpool Steven Gerrard da tsohon kyaftin din Chelsea Frank Lampard.

Uku daga cikin koci-koci 92 na kungiyoyin da ke gasar Premier da kungiyoyin da ke wasa a kasa da gasar ta Premier sun yi wa Ingila wasa.

Darektan horarwa na hukumar ta FA, Dan Ashworth, ya ce, suna matukar sha'awar samar da koci-koci 'yan Ingila, wadanda za su yi aiki da tawagogin wasan kasar.

Ko kuma wadanda za su koma cikin gasar Premier ko kungiyoyin kasa da Premier.

A kan hakan ya ce akai akai yana tuntubar wasu daga cikin tsoffin 'yan wasan Ingila da ma wadanda ke buga wa kasar yanzu a kan shirin horar da koci-kocin da ake son farawa.

A game da Scholes jarrabawar da ake yi masa za ta nuna ko zai iya koyar da 'yan wasa yadda ake bayar da kwallo, saboda abin da ya kware da shi ne a lokacin yana wasa.

Tsawon lokacin da duk wanda za a ba horon kocin zai yi ya danganta da kokarinsa, domin akwai wasu abubuwan da za a bukaci su kammala kafin a tabbatar da kwarewarsu.

A yanzu haka dai Scholes yana samun horon tabbatar da kwarewarsa a kungiyar Blackburn.