Fifa ta ci tarar Ingila da Scotland da Wales da Ireland ta Arewa

'yan wasan Ingila a lokacin haduwarsu da na Scotland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Ingila da Scotland sun daura bakin kyalle mai alamar jan fure na tunawa da sojin da suka mutu na yakin duniya na daya a hannunsu

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta ci tarar hukumomin yankuna hudu na tarayyar Birtaniya saboda sanya alamar tunawa da sojin da suka mutu a yakin duniya na daya da 'yan wasansu suka yi.

Fifa ta ci tarar su ne saboda 'yan wasan sun daura alamar a hannuwansu a lokacin wasannin neman cancantar zuwa gasar kofin duniya, lokacin da ya zo daidai da ranar tunawa da 'yan mazan jiyan.

'Yan wasan Ingila da na Scotland sun sanyi alamar ne mai kamannin fure da launin ja a lokacin wasansu a Wembley ranar 11 ga watan Nuwamba.

Haka su ma 'yan Wales da Ireland ta Arewa a lokacin wasanninsu na neman samun damar zuwa gasar ta duniya sun sanya alamar ko a filin wasa ko a wurin 'yan kallo.

Fifa ta ci tarar Ingila fan 35, 311, sannan ta ci tarar Scotland da Wales fan 15, 694 yayin da ta ci tarar Ireland ta Arewa fan 11,770.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Dan wasan Ingila sanye da alamar tunawa da sojin Birtaniya da suka mutu a yakin duniya na daya

A shekarar 2011 Fifa, ta amince wa 'yan wasan Ingila da Scotland da Wales su sanya alamar a lokacin wasanninsu na watan Nuwamba da suka zo daidai da ranara tunawa da sojojin na yakin duniya na daya.

To amma a wannan shekarar Fifa din karkashin jagorancin sabon shugabanta Gianni Infantino, ta hana su sanya alamar, kuma ta ce za ta hukunta su idan suka ki yarda.

Ita dai Fifa ta hana 'yan wasan yankunan hudu na Birtaniya sanya alamar ne a lokacin wasannin domin a cewarta, abu ne na siyasa.

Kuma a dokokinta ta hana yin amfani da wata alama ta addini ko siyasa da sauran abubuwa makamantansu da ke nuna wani bangaranci a wasanninta.

Hukumomin kwallon kafa na yankunan hudu na tarayyar Birtaniya suna nazari a kan hukuncin kafin su san abin da za su yi a kai, walau daukaka kara ko kuma su biya.