Super Falcons sun kawo karshen zaman dirshan

Super Falcons na murnar daukar kofin Afirka karo na takwas

Asalin hoton, DARIUS MEKE

Bayanan hoto,

Kudin da kowace 'yar wasa ya kamata ta samu ya wuce naira miliyan goma

'Yan wasan kwallo kafa mata na Najeriya sun kawo karshen zaman dirshan din da suke yi a otal a Abuja, bayan da aka biya su kudaden da suke bin gwamnati.

'yan wasan sun shiga zaman dirshan ne a otal din, a kan kin biyan kowacce daga cikinsu dala 23,650, kudaden da ya kamata a ba su na cin kofin kasashen Afirka na 2016 a Kamaru.

Daya daga cikin 'yan wasan ta tabbatar wa da BBC cewa, ita da wadda suke daki daya a otal din sun samu kudadensu.

Tun bayan dawowarsu daga Kamarun ne suka ki barin otal din har sai an biya su kudade, wadanda a lokacin hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce ba ta da kudin a lokacin.

Hakan ne ya kai ga a rana ta 10 ta korafin nasu, suka yi zanga-zanga zuwa majalisar dokokin kasar a daidai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ke gabatar da kasafin kudin kasar na 2017 a majalisar.

Daga nan kuma suka nufi fadar shugaban kasar, inda shugaban ma'aikata na fadar Mallam Abba Kyari, ya karbe su tare da yi musu alkawarin cewa gwamnati za ta shawo kan matsalar.

Kazalika daga baya kuma Shugaba Buhari ya bayar da umarnin a biya 'yan wasan, duk kudaden da suke bi.

Abin da ya kai gwamnati ta ba wa hukumar kwallon kafar ta Najeriya dala miliyan 1.2 domin biyan 'yan wasan kudaden.

Nasarar ta Najeriya a Kamaru ita ce ta takwas, wanda hakan ke nufin sau biyu ne kawai ba su dauki kofin ba tun da aka fara gasarsa a 1998.

Daga kudin ne kuma aka biya bashin da 'yan wasan kasar maza da suka yi wasannin neman cancantar zuwa gasar kofin duniya ta 2018 bashin da su ma suke bi.