Origi: Liverpool za ta je yaki ne Everton

Divock Origi da Adam Lallana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Divock Origi ne ya fara cin kwallo lokacin da Liverpool ta ci Everton 4-0 a Anfield a watan Afrilu lokacin da suka hadu na karshe

Liverpool za ta tunkari wasanta na mako na 17 a gidan Everton Goodison Park, ranar Litinin kamar yaki in ji Divock Origi.

Dan wasan na gaba na Liverpool dan Belgium, ya ce, suna son su yi nasara a wasan, amma sun san ba abu ne mai sauki ba, domin karawa ce ta hamayya.

Origi wanda ya ci kwallo a wasanni biyar da ya yi a baya ya ce dole ne mu shirya wasan da kyau.

Kyaftin din Liverpool Phil Jagielka ba zai buga wasan na Litinin ba saboda hukuncin hana shi wasa daya da aka yi.

Kocin kungiyar Jurgen Klopp ya ce kila ya sa Daniel Sturridge, bayan jiyyar da ya yi ta ciwon da ya ji a guiwa.

Bajamushen ya kuma tabbatar da cewa Simon Mignolet ne zai tsare musu raga, bayan da ya maye gurbin Loris Karius, a wasan da Middlesbrough ta ci su 3-0.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Romelu Lukaku ya ci kwallo biyar a wasa takwas na Premier da ya yi a haduwarsu da Liverpool

Liverpool za ta yi wasan ne da maki tara tsakaninta da ta daya a tebur Chelsea, wadda ta yi nasararta ta 11 a jere, da ci 1-0 a gidan Crystal Palace.

Everton na neman nasararta ta biyu a jere ta zama ta bakwai a tebur, sai dai sau daya kawai ta taba yin nasara a haduwarsu 19 da makwabtan nata, shekara shida baya, a Oktoban 2010.