Arsenal ta kama hanyar saryar da damarta a Premier kamar a baya kenan?

Arsene Wenger da Pep Guardiola

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Arsene Wenger kamar a wasan Everton ya dora alhakin doke su a kan alkalin wasa

A ranar Lahadi ne Arsenal wadda ta fara jefa kwallo a ragar Manchester City a Etihad ta yi sake har masu masaukin bakinta suka rama kwallon suka kara ta biyu aka tashi 2-1.

A lokacin wasan na mako na 17, magoya bayan Man City, sun yi amfani da wakar da magoya bayan Arsenal suke amfani da ita su karya lagon abokan karawarsu, a lokacin Gunners na cikin kungiyoyin da ba a barinsu a baya wurin cin kofi.

A wancan lokacin Arsenal din na karkashin jagorancin George Graham, da kuma lokacin da Arsene Wenger yake kan ganiyarsa, inda suke daukar kofi ba kakkautawa.

Rashin nasarar na ranar Lahadi shi ne karo na biyu a cikin sati da reshe yake juyewa da mujiya ga Arsenal din a doke ta, mummunar dokewa, bayan ta fara cin kwallo.

Arsenal ta kasance a gaba da kwallo dayar da take fara ci a wasanta a gidan Everton da kuma Manchester City, kafin daga baya a rama a kuma kara mata daya, sannan kuma a fi karfinta a duk wasannin biyu.

Wannan ya kan zama wata alama ta dusashewar Arsenal a gasar ta Premier ga wadanda suka saba ganin irin hakan a baya.

To kenan za a iya cewa wasan na Lahadi da ta wuce alama ce ta tabbatar da maganar da akan yi ta sammakon bubukuwa, ko wadda a kan ce ta yaro kyau take ba ta karko ga Arsenal da Wenger?

Kuma kasancewar a tashin farko Arsenal din takan kasance ta daya ko kuma cikin na gaba-gaba a tebur, amma idan tafiya ta fara nisa sai a bar ta a baya?