Liverpool ta koma ta biyu bayan ta doke Everton 1-0

An dakata da wasa saboda an jeho abin sa hayaki lokacin murnar 'yan Liverpool

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An jeho abin da ke tayar da hayaki cikin fili lokacin da 'yan Liverpool ke murnar kwallon da suka ci

Liverpool ta kawar da Manchester City ta koma matsayi na biyu a teburin Premier bayan da ta bi abokan hamayyarta Everton har gida ta doke su 1-0.

Sadio Mane ne ya zura kwallon a ragar Everton a minti na hudu cikin takwas da alkalin wasa ya kara bayan minti 90.

An kara tsawon lokacin ne saboda jinkirin da aka rika samu na katin gargadi da alkalin wasa ya rika bayar wa kan ketar da 'yan wasan ke yi.

Kafin Mane ya ci kwallon Daniel Sturridge ne ya yi wata 'yar gala-gala da 'yan wasan baya na Everton, sannan ya shari kwallon ta doki sandar raga ta dawo,.

Nan da nan kamar yadda ya saba sai Mane bai yi wata-wata ba ya kutsa cikin 'yan wasan Everton da gudu ya shirga ta a raga.

Yanzu Liverpool ta kawar da Manchester City daga matsayin na biyu, inda take da maki 37, yayin da City ta koma ta uku da maki 36.

Ita kuwa Everton tana nan a matsayinta na tara da maki 23.

Wannan shi ne karon farko da Mane ya buga wannan wasa na hamayya tsakanin kungiyoyin biyu.

Alkalin wasa ya dakatar da wasan na dan lokaci bayan da aka jeho wani abu mai sa hayaki cikin fili, lokacin da L'yan Liverpool ke murnar kwallon da suka ci.