Leicester ta daukaka kara kan korar Vardy

Alkalin wasa na ba wa Jamie Vardy jan kati a wasansu da Stoke

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jan katin shi ne na biyu da aka ba wa Vardy a 2016

Leicester City ta daukaka kara a kan jan kati na kora da alkalin wasa ya ba wa dan wasanta na gaba Jamie Vardy a wasan da suka yi canjaras 2-2 da Stoke.

Alkalin wasa ya kori Vardy ne a minti na 28 kan yadda kafa bibbiyu ya durar wa Mame Diouf a wasan na Premier na ranar Asabar.

Idan kungiyar ba ta yi nasara ba a daukaka karar, dan wasan na Ingila mai shekara 29 ba zai buga wasa uku ba.

Wasannin da ba zai buga ba su ne wanda Leicester za ta yi da Everton da West Ham da kuma Middlesbrough.