An haramta wa Shelvey wasa biyar

Jonjo Shelvey a lokacin wasan

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Kila Jonjo Shelvey ba zai sake buga wa Newcastle wasa ba sai a ranar 21 ga watan Janairu da Rotherham

Wani kwamiti mai zaman kansa ya haramta wa dan wasan tsakiya na Newcastle Jonjo Shelvey yin wasa biyar bayan samunsa da laifin amfani da kalaman batanci na wariyar launin fata.

An kuma ci tararsa fan dubu 100 tare da umartarsa ya halarci ajin darasin hukumar kwallon kafa ta Ingila na koyar da da'a.

Shelvey, mai shekara 24, ya bukaci a ba shi dama ya kare kansa da kansa domin ya kalubalanci hukuncin.

An dai yi masa hukuncin ne saboda abin da ya faru tsakaninsa da dan wasan Wolves Romain Saiss, a wasan da Necastle suka yi rashin nasara 2-0 ranar 17 a watan Satumba.

Dan wasan na tawagar Ingila yana da kwana bakwai ya daukaka kara.

A sanarwar da ta fitar kungiyar Newcastle ta ce za ta saurara ta ga rubutaccen dalilin hukumar kwallon kafa ta Ingila na hukuncin, kafin ta ce wani abu a kan lamarin.

Za a jinkirta hukuncin na hukumar ta FA kafin a saurari daukaka kara kan hukuncin.