Scotland za ta gina filayen tennis saboda girmama Andy Murray

Andy Murray ya zama gwarzon wasanni na shekara ta 2016 na BBC

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Hukumar Tennis ta Scotland na son dorawa a kan nasarorin Andy Murray

Za a bunkasa wasan tennis a Scotland da fan miliyan 15, inda za a linka rufaffun filayen wasan zuwa 225 nan da shekara 10, tare da karfafa wa mutane guiwa su rika shiga wasan, ganin yadda Andy Murray, dan yankin ya yi suna a duniya.

Shugaban hukumar kwallon tennis na yankin Michael Downey ya ce lokaci ne da ya kamata a yi amfani da damar da aka samu daga nasarorin Andy Murray da dan uwansa Jamie Murray.

Ya ce, dole ne mu kirkiri wani abu da za a dade ana tunawa da shi ga Scotland.

Shi kuwa shugaban hukumar wasanni ta sportscotland Mel Young yana fatan matakin zai kara yawan masu yin wasan na tennis.

Gwarzan wasanni na shekara na BBC Andy Murray mai shekara 29, ya kasance na daya a duniya na shekara ta 2016, bayan ya ci gasar Wimbledon da kuma ta ATP Tour ta wannan shekara.