An hana Vardy wasa uku

Alkalin wasa Craig Pawson na ba wa Vardy jan kati

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bayan wasan kocin Leicester Ranieri ya ce Vardy kwallo ya yi niyyar nema ba keta ba

Dan wasan Leicester Jamie Vardy ba zai buga wasa uku ba, saboda rashin nasarar da kungiyar ta yi a daukaka karar jan katin da alkalin wasa ya ba shi a wasan da suka yi 2-2 ranar Asabar da Stoke.

Alkalin wasa ya kori dan wasan mai shekara 29 wanda yake ikirarin cewa an kore shi ne bisa kuskure, ikirarin da hukumar kwallon kafar ta Ingila ta yi watsi da shi.

Yanzu dai Vardy ba zai yi wasan da Leicester za ta yi da Everton da West Ham da kuma Middlesbrough ba.

Alkalin wasa Craig Pawson ya ba wa dan wasan gaban na Ingila jan kati a minti na 28 saboda ketar da ya yi wa Mame Diouf kafa bibbiyu.