Fifa za ta kara hukunta Amos Adamu na Nigeria

Amos Adamu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amos Adamu ya yi ta musanta zargin cin hancin da Fifa take masa

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, za ta kara hukunta jami'in harkokin wasanni na Najeriya Dakta Amos Adamu da haramcin shiga harkokin wasannin kwallon kafa na shekara biyu.

Tun a watan Maris na 2015 ne masu bincike na kwamitin kula da da'a na Fifa din ke binciken zargin saba ka'idojin hukumar da aka yi wa Amos Adamu.

Bayan da masu binciken suka kammala aiki, sun bayar da shawarar a haramta wa tsohon dan kwamitin zartarwa na Fifa shiga harkokin wasan kwallon kafa na tsawon shekara biyu tare da cin tararsa wasu kudade.

Tun a shekara ta 2010 daman Fifa din ta hukunta tsohon jami'in dan Najeriya, da haramcin shiga harkokin wasanni tsawon shekara uku.

Za dai a dauki watanni kafin a yanke shawara kan wannan hukunci na yanzu da masu binciken na Fifa suka bayar da sahawara a yi masa.

Dakta Amos Adamu mai shekara 62 wanda ya taba kasancewa dan hukumar zartarwar hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF, tsohon dan hukumar zartarwar Fifa ne tsawon shekara hudu.

A 2010 ne aka same shi da laifin neman a ba shi kudi a zaben kasar da za a ba wa damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya, zargin da ya musanta.

A watan Oktoba na 2013 ne hukuncin dakatarwar ya kare

A da ana daukar Dakta Amos Adamu, wanda babban jami'in harkokin wasanni ne a Najeriya tsawon shekara 20, a matsayin wanda zai iya gadar dadadden shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka, Issa Hayatou.