Kofin Afirka: 'Yan wasan Kamaru sun bijire wa kasarsu

'Yan wasan Indomitable Lions na Kamaru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan wasan sun ce suna gudun rasa wurarensu ne a kungiyoyinsu na Turai

Wasu 'yan wasan Kamaru 7 sun ce ba sa son zuwa gasar cin kofin Afirka da za a fara a watan Janairu a Gabon, domin mayar da hankali kan kungiyoyinsu.

Hakan zai iya sa hukumar kwallon kafa ta kasar ta sa kafar wando daya da su, wanda kuma zai iya kai wa ga hana su yi wa kungiyoyin nasu wasa a lokacin gasar har zuwa 6 ga watan Fabrairu da za a kare gasar.

Joel Matip na Liverpool na daya daga cikinsu, kuma ya gaya wa kocin Kamarun Hugo Broos cewa ba sa sha'awar a sa su a tawagar wasan da za a yi a Gabon, wadda za a fara ranar 14 ga watan janairu.

Kocin ya mayar da martani da cewa, 'yan wasan sun fifita bukatarsu kan ta tawagar kasarsu, kuma hukumar kwallon kasar tana da damar daukar matakin da ya dace kamar yadda dokokin Fifa suka tanada.

Sauran 'yan wasan shida su ne Andre Onana na Ajax Amsterdam da Guy Roland Ndy Assembe na Nancy da Allan Nyom na West Brom.

Ragowar su ne Maxime Poundje na Girondins Bordeaux da Andre-Frank Zambo Anguissa na Olympique Marseille da kuma Ibrahim Amadou na Lille.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A farkon watan nan an sanya dukkanin 'yan wasan bakwai a jerin sunayen 'yan wasa 35 na farko da za tace wadanda za su je gasar, wadda Kamarun take rukuni na daya(Group A), da masu masaukin baki, Gabon da Burkina Faso da kuma Guinea Bissau.

Shi dai Matip ba ya son yi wa kamaru wasa ne saboda yadda bai ji dadin lamarin ba a baya tsakaninsa da masu horad da tawagar, kamar yadda sanarwar ta ce.

Dan wasan haifaffen Jamus bai buga wa Kamaru wasa ba tun lokacin gasar kofin duniya da aka yi a Brazil, amma kocin wanda ya karbi aiki a watan Fabrairu, sau biyu yana zuwa ya gana da shi, domin ya shawo kansa ya dawo buga wa Kamarun wasa.

Shi kuwa Nyom ya gaya wa kocin yana son ya tsaya a West Brom domin ya tabbatar da dorewar wurinsa a kungiyar.

Haka su ma Amadou da Ndy Assembe da Onana da kuma Zambo Anguissa suka ce.

Shi kuwa Poundje wanda bai taba yi wa Kamaru wasa ba, ya ce ya fi son ya buga wa Faransa wasa ne.

A mako mai zuwa ne Kamarun za ta bayyana sunayen tawagar 'yan wasa 23 da za ta je gasar da su.