Premier: Ka san kungiyar da ta yi wasa 55 dan Ingila bai ci mata kwallo ba?

'Yan wasan Stoke City na murnar cin kwallo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan wasan Stoke City na murnar cin kwallo, amma ba dan Ingila ba ne ya ci

Ko za a iya cewa Stoke City kungiya ce da ba ta da sakaci da saurarawa wadda kuma ke da kishi ga al'adar kwallon kafar Ingila? To ba dai Stoke City ta koci Mark Hughes ba.

Ka san cewa wasan da ta yi canjaras 2-2 da Leicester na ranar Asabar, shi ne na 55 na Premier, rabon da wani dan wasa dan Ingila ya ci mata kwallo, abin da ya ta kamo Newcastle a wannan matsayi?

Kwallon da Peter Crouch ya ci wa kungiyar a minti na 86, a lokacin da suka casa Liverpool 6-1 ranar 24 ga watan Mayu na 2015, ita ce ta karshe da wani dan Ingila ya ci mata a Premier.

Ita kuwa Newcastle ta kawo karshen kasancewa da wasa 55 da take cin kwallo ba tare da wani dan Ingila ya ci mata ba, a lokacin da Steven Taylor ya ci a wasan da suka doke Cardiff 3-0 a watan Mayu na 2014.

To amma kuma Arsenal ce ke rike da kambin cin kwallo ba tare da wani dan wasa dan Ingila ya ci ba, inda take da wasanni 97.

Ta kawo karshen hakan ne a lokacin da Theo Walcott ya ci mata kwallo suka tashi 2-2 da Birmingham a watan Fabrairu na 2008.

Asalin hoton, Elvis

Bayanan hoto,

Kocin Stoke City Mark Hughes

A makon nan cikin fitattun 'yan wasa 11 na Stoke, wadanda suka yi mata wasa, ban da mai tsaron raga, guda biyu ne kawai 'yan Ingila ;Ryan Shawcross da Glen Johnson.

Kuma rabon da wani daga cikinsu ya ci mata kwallo tun watan Janairu na 2015, inda Shawcross ya ci.