Kun san dalilin da Chelsea ke son zama ta daya a tebur duk ranar Kirsimeti?

Chelsea sun dauki kofin Premier
Bayanan hoto,

Duk kakar da Chelsea ta dauki kofunan Premier ta kasance ta daya a tebur ranar Kirsimeti

Kamar a wasu shekarun baya na Premier, Chelsea za ta kasance zaune daram a kan teburin gasar Premier ba tare da wata fargaba ba a ranar Kirsimeti.

Wannan dai wata alama ce ta alheri ga 'yan wasan na Antonio Conte, domin sun kasance a irin wannan matsayi ne a duk lokuta hudun da suka dauki kofin. Premier.

Chelsea ta dauki kofin a kakar 2004-05 da 2005-06 da 2009-10 da kuma 2014-15.

Sai dai kuma a cikin kashi dari da kungiyar take kasancewa a kan tebur ranar Kirsimeti, kashi 50 ne kawai take yin nasarar cin kofin a tarihin gasar, wato sau 12 daga cikin 24.

To amma kuma sabanin wannan al'ada ko camfi, Arsenal ba ta taba kasancewa jagora a teburin na Premier ba, a duk kakar da ta dauki kofunanta uku.

Arsenal ta dauki kofin na Premier ne a kakar1997- 98 da 2001-02 da kuma 2003-04.

Babban sabanin alherin zama a kan teburin na Premier ranar Kirsimeti ga wata kungiya ya faru ne a kan Aston Villa a kakar 1998-99, lokacin da ta fado daga matsayi na daya zuwa na shida.

Liverpool ce ta fi rashin nasarar amfana da wannan dama ta kasancewa a kan tebur ranar Kirsimeti, da ake gani alama ce ta alheri, ta dauki kofin gasar.

Hakan ya kasance ne domin sau uku tana samun wannan dama amma kuma sai ta kasa daukar kofin.

A daya bangare na teburin Premier, wato karshen kenan, magoya bayan Hull City na cike da bakin ciki.

Saboda duk tsawon kakar ba su fado kasa ba, sai a ranar Asabar, inda West Ham ta doke su, abin da ya sa za su kasance a karshen tebur ranar Kirsimetin.

A tarihi kungiyoyin da suka kasance a karshen teburin Premier ranar Kirsimeti, a kaka 24, a 21 kungiyoyin sun fadi daga gasar.

Kungiyoyin da kadai suka kasance a karshen teburi ranar Kirsimeti kuma ba su fadi daga gasar ba, su ne West Brom 2004-5 da Sunderland 2013-14 da kuma Leicester 2014-15.