Tarihin da jan katin Jamie Vardy ya kafa a Premier

Alkalin wasa na ba wa Jamie Vardy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jamie Vardy ya zama dan wasa na biyu da aka ba wa jan kati biyu a 2016

Za a iya cewa jan katin da allakin wasa ya ba wa Jamie Vardy saboda ketar da ya yi wa Mame Diouf a wasan da Leicester ta yi canjaras da Stoke ranar Asabar, bai kamata ba.

Amma kuma abu daya da ba za a iya musantawa ba shi ne, dan wasan ne na biyu da ya samu jan kati a gasar Premier a 2016.

Daya dan wasan shi ne Victor Wanyama, wanda alkalin wasa ya kora a watan janairu da Fabrairu, kafin ya bar Southampton ya koma Tottenham.

Jamie Vardy ya fara samun jan kati ne a bana a wasan Leicester da West Ham wanda suka yi 2-2, a lokacin da alkalin wasa yake ganin ya fadi da gangan domin neman fanareti.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lokacin da Jamie Vardy ya fadi a da'irar gidan West Ham, abin da ya jawo masa jan kati na farko

'Yan wasa hudu ne kawai a tarihi suka taba samun jan kati sau uku a kaka daya:

Vinnie Jones - 1995

Dion Dublin - 1997

Franck Queudrue - 2002

Lee Cattermole - 2010

Duk da haka ba za a manta da Granit Xhaka na Arsenal, wanda alkalin wasa ya kora sau uku a kungiyar Borussia Monchengladbach a gasar Bundesliga ta Jamus a 2015.