Man Utd na son Mourinho ya cigaba har 2025

Jose Mourinho lokacin da Man United ta dauke shi koci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zuwa yanzu wata shida kawai Mourinho ya yi a kwantiragin shekara uku da United

Manchester United na son Jose Mourinho ya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa 2025, duk da cewa wata shida kadai kocin ya yi a cikin kwantiraginsa na shekara uku in ji jaridar Star.

Dan wasan tsakiya na Wolfsburg, dan Jamus, Julian Draxler mai shekara 23 wanda a baya Arsenal ke zawarcinsa, ya amince ya tafi wurin zakaraun Faransa, PSG a kan fan miliyan 34 kamar yadda Daily Mail ta ruwaito.

West Ham za ta nemi aron ko dai dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 19, ko dan wasan gaba na Faransa Anthony Martial, mai shekara 21, daga Manchester United a watan Janairu mai kamawa in ji Telegraph.

Manchester United na tattaunawa da Atletico Madrid domin sayen dan wasanta na gaba, dan Faransa Antoine Griezmann mai shekara 25 a kan sama da fan miliyan 60 in ji Sun.

Haka kuma United a shirye take ta biya fan miliyan 50 domin sayen 'dan wasan baya na Benfica, dan Sweden Victor Lindelof mai shekara, 22 kamar yadda jaridar Mirror ta labarto

Arsenal kuwa tana sha'awar sayen dan wasan Valencia, dan Spian Jose Gaya mai shekara 21 in ji Mirror.

Real Madrid ta gabatar da dan wasanta, na tsakiya dan Colombia James Rodriguez mai sheakara 25-year ga kungiyoyin Premier, in ji Daily Mail.

Manchester United na tattaunawa domin sayen dan wasan Benfica Nelson Semedo mai shekara 23 in ji Record.

Arsenal na sha'awar sayen mai tsaron ragar Standard Liege Guillaume Hubert mai shekara 22 na tawagar 'yan wasan kasa da shekara 21 na Belgium in ji Daily Mail.

Shi kuwa dan wasan Manchester United, dan Ingila Ashley Young, mai 31, kungiyoyin Watford da Everton da Swansea da West Brom da Burnley da kuma Hull City ne ke nemansa in ji Sun.

Wadannan wasu ne daga cikin labaran saye da sayar da 'yan wasa da jaridun Birtaniya da sauran kafofin yada labarai na Turai suka ruwaito.