An fitar da jadawalin gasar Zakarun Afirka

Hukumar kwallon Afirka ta sake tsarin gasar ta Zakarun Afirka a bana
Bayanan hoto,

Hukumar kwallon Afirka ta sake tsarin gasar ta Zakarun Afirka a bana

An fitar da jadawalin gasar cin kofin Zakarun nahiyar Afirka na kwallon kafa da aka yi a birnin Alkahira na Masar ranar Laraba.

An ba wa masu rike da kofin, Mamelodi Sundowns na Afirka ta Kudu damar tafiya kai tsaye zuwa zagaye na biyu na gasar, bisa sabon tsarin gasar da aka bullo da shi.

Haka su ma tsooffin zakarun gasar TP Mazembe na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo, da kuma manyan kungiyoyin Masar biyu Zamalek da Al Ahly, duk sun samu wannan damar.

A sabon tsarin za a yi zagaye biyu na neman shiga gasar kafin a je zagayen 'yan 16, abin da ya linka wasannin shekarar da ta wuce sau biyu.

Kungiyoyi 46 ne za su yi wasannin matakin farko, wadanda za a fara ranar 10 zuwa 12 ga watan Fabrairu