Boksin: 'Dole ne Pulev ya dambata da Joshua ko Klitschko'

Wladimir Klitschko dan Ukrain da Anthony Joshua dan Birtaniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shekarar Wladimir Klitschko dan Ukrain 40, shi kuwa Anthony Joshua 27

Masu hada damben boksin 'yan jamus Kalle da Nisse Sauerland sun tabbatar da cewa dole ne dan dambensu Kubrat Pulev ya kara da wanda ya yi nasara a damben Anthony Joshua da Wladimir Klitschko.

Mai rike da kambin ajin masu nauyi na hukumar boksin ta duniya ta IBF, Joshua zai gwambza da Klitschko a filin wasa na Wembley ranar 29 ga watan Afrilu.

Kuma bayan damben nasu, duk wanda ya yi nasara ya samu kambin, dole ne ya yarda ya fafata da dan damben boksin din na Bulgaria a cikin kwana 90.

Sai dai kuma idan har Joshua da Klitschko suka ce za su sake dambatawa tsakaninisu, maimakon fuskantar Pulev, to za a iya kwace kambin daga duk wanda ya yi nasarar samunsa.

A irin wannan sharadin ne aka kwace wa Tyson Fury kambinsa bayan da ya kawo karshen kasancewar Wladimir Klitschko, dan Ukrain, a matsayin zakaran ajin masu nauyin.