Fifa: Guinea-Bissau ta fi kowacce kasa a Afirka cigaba a kwallon kafa

Kyaftin din Guinea-Bissau Bocundji Ca

Asalin hoton, Francois

Bayanan hoto,

Kyaftin din Guinea-Bissau Bocundji Ca da ke wasa a Faransa shi zai jagoranci kasar a Gabon

Guinea-Bissau ta samu cigaba fiye da kowace kasar Afirka a jerin Fifa na kasashen da suka fi iya kwallon kafa na 2016, inda ta wuce matsayi 78 tun watan Disamba na bara.

A jadawalin da hukumar kwallon kafar ta duniya, Fifa, ta fitar na wannan watan na Disamba Guinea-Bissau ce ta 68 a duniya kuma ta 15 a Afirka.

Hakan na nufin yanzu ta wuce Uganda da Togo da kuma Zimbabwe wadanda dukkaninsu sun samu gurbin gasar cin kofin Afirka ta 2017 da za a yi a Gabon.

Senegal ta kawo karshen shekarar a matsayin kasar da ta fi kowacce a Afirka iya kwallon, kuma ita ce ta 33 a duniya.

Guinea-Bissau ta samu damar zuwa gasar cin kofin Afirka ne a karon farko, bayan da ta doke Kenya da Zambia a 2016.

Duk da cewa Congo-Brazzaville ta doke ta a wasansu na karshe na neman gurbin gasar ta Afirka, duk da haka ta kammala a matsayi na daya a rukuninsu ta samu damar zuwa Gabon din.

A duniya gaba daya kuwa Argentina ta ci gaba da zama ta daya a jerin gwanayen tamaular.

2) Brazil (3) Germany, (4) Chile (5) Belgium (6) Colombia (7) France (8) Portugal (9) Uruguay (10) Spain (11) Switzerland (12) Wales (13) England

Ga jerin sunayen kasashen Afirka 10 da suka fi kwazo a fagen kwallon kafar na watan Disamba (matsayinsu na duniya a cikin baka):

Senegal (33)

Ivory Coast (34)

Tunisia (35)

Egypt (36)

Algeria (38)

DR Congo(48)

Burkina Faso (50)

Nigeria (51) (ba ta samu gurbin zuwa Gabon ba)

Ghana (53)

Morocco (57)

Sauran kasashen da suka samu gurbin gasar cin kofin Afirka ta 2017:

11 Mali (60)

13 Cameroon (65)

15 Guinea-Bissau (68)

18 Uganda (72)

23 Togo (91)

29 Zimbabwe (102)

34 Gabon (110)