Chelsea za ta sayo 'yan Monaco biyu da kudin Oscar

Oscar ya yi sallama da Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea za ta sayo 'yan wasan da kudin cinikin Oscar wanda shi kuma zai iya samun kusan fan dubu 400 a mako a China

Wasu rahotanni na nuna cewa kocin Chelsea Antonio Conte zai yi amfani da fan miliyan 60 da suka samu a cinikin sayar da Oscar ga Shanghai domin sayo 'yan wasa biyu daga Monaco.

Kamar yadda rahotannin suka nuna 'yan wasan biyu da Chelsea ke son saye daga kungiyar ta Faransa su ne Tiemoue Bakayoko da Dijibril Sidibe.

Kocin na Chelsea ya yi tattaki zuwa Faransa tare da darektan kwallon kafa na kungiyar Michael Emenalo domin ganin yadda Bakayoko da Sidibe suke taka leda

Bakayoko dan wasan tsakiya da kuma Sidibe, dan wasan baya sun taka leda a wasan da Tottenham ta yi da Monaco na gasar cin Zakarun Turai, ranar 22 ga watan Nuwamba, na 2016.