Crystal Palace ta kori Alan Pardew

Asalin hoton, Getty Images
A watan Janairu na 2015 ne Alan Pardew ya koma Crystal Palace ha horar da tamaula
Crystal Palace ta kori kocinta Alan Pardew bayan kusan shekara biyu a kungiyar, inda yanzu take matsayi na 17 a teburin Premier.
A wasanni goma sha bakwai na gasar Premier da kungiyar ta yi a bana, an doke ta a goma, ta ci hudu, sannan ta yi canjaras a uku.
Sannan an zura mata kwallo 32 a raga yayin da ta jefa 28, kuma tana da maki 15 a wasannin bana.
Kungiyar ta dauki Pardew a kwantiragin shekara uku da rabi a watan Janairu na 2015, amma kuma ta kori kocin mai shekara 55 bayan nasara daya a wasanni 11.
Palace ta samu maki 26 ne kawai a wasannin Premier 36 da ta yi a shekarar 2016, kuma maki daya ne kawai tsakaninta da rukunin faduwa daga gasar a yanzu.
Masu lura da harkokin wasan kwallo kafa na ganin Sam Allardyce a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
A sanarwara da ya bayar game da korar tasa, Pardew, ya ce, yana matukar kaunar kungiyar ta kwallon kafa, kuma yana takaicin yadda lokacinsa ya zo karshe a kungiyar.
A lokacin da yake wasa Pardew ya buga wa kungiyar wasanni sama da 100, tsakanin 1987 da 1991, kuma ya kai ta wasan karshe nma kofin kalubale na FA a bara.
Kawo yanzu kungiyar ba ta sanar da wanda zai jagorance ta ba a wasan Premier da za ta yi a gidan Watford ranar 26 ga watan Disamba.