Lloris ya sabunta kwantiragi a Tottenham

Asalin hoton, Getty Images
A tsohon kwantiragin Lloris Tottenham na biyansa fan dubu 80 a duk mako
Mai tsaron ragar Tottenham Hugo Lloris ya kulla sabuwar yarjejeniya ta ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekara ta 2022.
Golan mai shekara 29, wanda shi ne kyaftin din kungiyar, ya buga mata sama da wasanni 151 na Premier, tun lokacin da ta sayo shi daga Lyon a kan fan miliyan 7.8 a watan Agustan 2012.
Dan wasan na tawagar Faransa wanda a da ake biyansa albashin da ya kai fan dubu 80 a duk sati, da kwantiraginsa zai kare ne a 2019.
A lokacin da Lloris ya dawo kungiyar ya kulla yarjejeniyar shekara hudu ne, wadda alokacin Andre Villas-Boas ne ke kocinta.
Lyon tana da kashi 20 cikin dari na duk ribar da Tottenham za ta samu idan ta sayar da golan nata, Lloris.
A farkon watan nan ne dan wasan gaba na kungiyar Harry Kane, shi ma ya kulla sabon kwantiragi da zai ci gaba da zama a Tottenham din har 2022.