Afirka ta Kudu ta kori kocinta Mashaba

Asalin hoton, Getty Images
Tun watan Agusta na 2014 ne Ephraim 'Shakes' Mashaba yake aikin kocin Afirka ta Kudu
Afrika ta kudu ta kori kocin tawagar kwallon kafarta Ephraim Mashaba duk da ya jagoranci kasar ta doke Senegal a muhimmin wasanta na neman gurbin gasar Kofin Duniya a watan da ya wuce.
Wani kwamitin da'a da ya gudanar da bincike ya samu Mashaba da laifuka da dama, kan babatun da ya yi a kan shugaban hukumar kwallon kafar kasar Danny Jordaan da wasu bakinsa.
Kocin ya sha yin sa-in-sa da manyan jami'ai hukumar kwallon kafar ta Afirka ta Kudu (safa), a tsawon shekara hudu na aikinsa.