Rogers: Kwallo a fili mai ciyawar roba na bata wasa

Filin New Douglas Park mai ciyawar roba

Asalin hoton, SNS

Bayanan hoto,

A ranar Juma'a Celtic za ta yi wasa a filin New Douglas Park, mai ciyawar roba

Kocin Celtic Brendan Rodgers ya ce yana ganin fili mai ciyawar roba na bata wasan kwallon kafa, domin bai taba ganin wasa mai kyau da aka yi a kansa ba.

Rodgers ya ce yana ganin wannan shi ya sa kungiyoyi a Scotland, kamar Hamilton Academical, wadda za ta karbi bakuncinsu ranar Asabar suke zabar yin wasa a fili mai ciyawar roba maimakon mai ciyawar gaske.

Kocin ya ce shi dai har yanzu bai ga wani wasa da aka yi a filin mai ciyawar roba, wanda ya yi kyau ba.

Kuma ya ce duk kocin da ka tambaya zai gaya maka cewa, wasa a irin wannan filin daban yake.

Asalin hoton, SNS

Bayanan hoto,

Dan wasa Commons (a hagu) da Brendan Rogers

A bana Celtic ta yi wasa a irin wannan fili mai ciyawar roba, lokacin da ta doke Kilmarnock a filin Rugby Park.

kuma a lokacin Rodgers ya ce ba zai sauya tsarin 'yan wasansa ba saboda za a yi wasan a wannan fili.

says the playing surface will not influence his team selection.