Bilic: Sakho ba zai je gasar Afirka ba

Koci Slaven Bilin da Diafra Sakho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Slaven Bilic ya ce Sakho ba zai warke ba sai tsakiyar watan Fabrairu

Dan wasan West Ham da Senegal Diafra Sakho ba zai je gasar cin kofin kasashen Afirka ba ta 2017, saboda jinya da zai yi ta ciwon baya, ta karin mako takwas.

Ranar 30 ga watan Nuwamba, West Ham ta ce dan wasan mai shekara 26 ba zai yi wasa ba tsawon mako shida saboda raunin da ya ji a cinya, abin da ke nufin sai a tsakiyar watan Janairu zai dawo fili.

Amma kuma a ranar Alhamis din nan sai ga kocinsu Slaven Bilic yana cewa Sakhon zai cigaba da jinya har zuwa wasu makonni takwas, wato har zuwa tsakiyar Fabrairu kenan.

Wanda hakan ke nufin ba zai samu damar zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka ba, wadda za a fara ranar 14 ga watan Janairu.

Shekara biyu da ta wuce Sakho ya fice daga tawagar 'yan wasan Senegal saboda ciwon baya, amma kuma bayan kwana 18 ya ci wa West Ham kwallonta daya a wasan da ta doke Bristol City na kofin FA.

A kan haka hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta ci tarar kungiyarsa fan dubu 71.