An tace Aubameyang, Mahrez da Mane a zaben gwarzon dan kwallon Afirka

Dan Gabon da Borussia Dortmand Pierre-Emerick Aubameyang da lambar gwarzon Afirka na Caf na 2015

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, ne ya ci kyautar ta Caf a 2015

Dan wasan Borussia Dortmund da Gabon Pierre-Emerick Aubameyang zai iya sake zama gwarzon dan wasan Afirka na shekara, na hukumar kwallon kafar Afirka CAF domin ya kasance cikin guda uku da aka tace za a zabi na bana a cikinsu.

Dan wasan mai shekara 27 na takarar kambin ne da dan wasan Leicester dan Algeria Riyad Mahrez wanda ya samu kambin gwarzon dan wasan Afirka na shekarar 2016, na BBC, da dan Liverpool da Senegal Sadio Mane.

An tankade dan wasan Masar Mohamed Salah da Islam Slimani na Algeria bayan da suka kai matakin 'yan biyar.

Hukumar kwallon Kafar Afirkan, Caf, ta bayyana cewa za a sanar da wadanda suka yi nasara a wani biki da za a yi ranar Alhamis biyar ga watan Janairu a babban birnin Najeria, Abuja.

Nasarar da Aubameyang ya yi a shekarar da ta wuce ita ta kawo karshen mamayar da dan wasan Ivory Coast na Manchester City, Yaya Toure ke yi wa kambin sau hudu a jere.