Anis Amri: Mutumin da ya tattake mutane da mota a Jamus

Anis Amri: Mutumin da ya tattake mutane da mota a Jamus

Sama da mutum 12 ne suka mutu sannan wasu 50 suka samu raunuka a harin da aka kai a birnin Berlin na kasar Jamus.

Mahukuntan kasar sun saka ladan yuro 100,000 ga duk wanda ya bayar da bayanan da ya kai ga kama Anis Amri, dan kasar Tunisia da ake zargi da kai harin.