Ana ba da cin hanci wajen gayyatar 'yan Super Eagles

Nigerian Super Eagles
Bayanan hoto,

Amokachi ya ci wa Nigeria kofin nahiyar Afirka a 2014

Tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Nigeria, Daniel Amokachi, ya ce dabi'ar bai wa kociyan Nigeria kudi domin ya gayyaci dan kwallo ya zama ruwan-dare.

An dade ana zargin hakan na faruwa a Nigeria, duk da cewa babu wanda aka kama aka kuma tuhume shi kan lamarin.

Amokachi ya ce "A kodayaushe wakilan 'yan wasan tamaula suna bai wa mai horar da Super Eagles kudi domin a gayyaci dan kwallonsu, ko ya kamata da ake yin hakan?"

Tuni hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF, ta bukaci Amokachi da ya gabatar mata da shaida kan kalaman da ya yi.

Amokachi mai shekara 43, wanda ya ci wa Nigeria kofin nahiyar Afirka a shekarar 1994, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen matsalar da take tauye ci gaban kasar a fagen tamaula.

A baya can Amokachi ya yi aikin mataimakin kociyan Super Eagles karkashin Stephen Keshi a 2011-15 da Shaibu Adamu 2008-10 da Austin Eguavoen 2005-07.