Crystal Palace ta nada Allardyce sabon kociyanta

Crystal Palace

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Kwana daya tsakani da aka kori Pardew aka dauki Allardyce

Crystal Palace ta nada tsohon kociyan tawagar kwallon kafa ta Ingila, Sam Allardyce, a matsayin mai horar da 'yan wasanta domin maye gurbin Alan Pardew.

Palace ta kori Padew a ranar Alhamis bayan da kungiyar ke mataki na 17 a kan teburin Premier, inda ya ci wasa daya daga 11 da ya jagoranta.

Allardyce ya kulla yarjejeniyar aiki tare da Palace tsawon shekara biyu da rabi, bayan da ya gana da shugaban kungiyar Steve Parish.

Steve Parish ya ce "Sun yi murna da suka samu damar daukar mutum kamar Sam kwararren kociya".

Allardyce ya zauna bashi da kungiyar da yake jan ragama, tun bayan da hukumar kwallon kafa ta Ingila ta sallameshi daga jan ragamar tawagar kasar kwanaki 67 kan aikin.

Kociyan zai jagoranci atisayen da Palace za ta yi a ranar Asabar, sannan ya fuskanci wasan Premier da kungiyar za ta yi da Watford a ranar Litinin.