Kanin Bello da Shagon Dan Digiri sun yi canjaras

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Canjaras aka tashi tsakanin Ali Kanin Bello da Shagon Dan Digiri

Dambe 12 aka fafata a karawar da aka yi a ranar Lahadi da safe a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Daga cikin wasannin da aka dambata an yi kisa a gumurzu hudu, inda saura aka tashi canjaras, ciki har da wasan da ka yi tsakanin Ali Kanin Bello daga Arewa da Shagon Dan Digiri daga Kudu.

Wasannin da aka yi kisa sun hada da karawar da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa ya buge Dan Matawallen Kwarkwada daga kudu a turmi na biyu.

Da wasan da Soja daga Arewa ya buge Dogon Isya daga Kudu a turmin farko da wanda Shagon Caka-Caka daga Arewa ya doke Shagon Kugiya daga Kudu a turmin farko.

Dambe na karshe da ya yi kisa shi ne wanda Malam-Malam Shagon Kato Mai Karfi daga Kudu ya doke Shagon Dan Inda daga Arewa a turmin farko.

Wasannin da aka yi canjaras kuwa:

Bahagon Dogon Minista daga Kudu da Bahagon Maru daga Arewa

Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Shagon Sisco daga Kudu

Shagon Babangida daga Kudu da Shagon Buzu daga Arewa

Mahaukaci Teacher daga Arewa da Suda Shagon Kunnari daga Kudu

Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Bahagon Abba daga Arewa

Ali Kanin Bello daga Arewa da Shagon Dan Digiri daga Kudu

Shagon 'yan Sanda daga Arewa da Bahagon Dogon Auta daga Kudu

Shagon Dan Shariff daga Kudu da Bahagon Sunusi Dan Auta daga Arewa