Dambe hudu ne aka yi nasara daga guda 12 da aka yi a Abuja, Nigeria

Kimanin wasanni 12 aka dambata a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria, inda aka yi kisa a guda hudu daga cikinsu.

Daga cikin wasannin da aka dambata an yi kisa a gumurzu hudu, inda saura aka tashi canjaras,

Dambatawar da aka yi kisa ta hada da karawar da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa ya buge Dan Matawallen Kwarkwada daga kudu a turmi na biyu.

Da wasan da Soja daga Arewa ya buge Dogon Isya daga Kudu a turmin farko da wanda Shagon Caka-Caka daga Arewa ya doke Shagon Kugiya daga Kudu a turmin farko.

Dambe na karshe da ya yi kisa shi ne wanda Malam-Malam Shagon Kato Mai Karfi daga Kudu ya doke Shagon Dan Inda daga Arewa a turmin farko.