Premier: Liverpool ta koma ta 2 bayan doke Stoke 4-1

Asalin hoton, Rex Features
Adam Lallana ya ci wa Liverpool kwallo 4 ya bayar aka ci 4 a bana a Anfield
Liverpool ta sake kawar da Manchester City daga matsayi na biyu, kuma ta rage ratar da ke tsakaninta da Chelsea zuwa maki 6 bayan ta doke Stoke 4-1 a Premier.
Jon Walters ne ya fara ribatar raunin masu masaukin bakin a baya, inda ya ci wa Stoke City kwallonta daya a minti 12 da fara wasa.
To amma Adam Lallana ya rama wa Liverpool a minti na 34, kafin kuma minti goma tsakani Roberto Firmino ya kara cin bakin.
Bayan hutun rabin lokaci ne kuma G. Imbula ya ci kansu a minti na 59, yayin da Daniel Sturridge ya ci ta hudu a minti na 70.
Liverpool yanzu tana da maki 40 a gaban Manchester City mai maki 39, wadda za su kara da ita ranar jajiberin sabuwar shekara.
Kwallon da Daniel Sturridge, ya ci, ita ce ta farko a Premier a bana, kuma ita ce ta Liverpool ta 100 a karkashin jagorancin koci Jurgen Klopp.