Kofin Afirka: Zaha ya yi watsi da Ingila

Zaha ya yi watsi da Ingila , ya koma Ivory Coast

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zaha ya buga wa Crystal Palace wasa 19 a bana, kuma ya ci kwallo uku

An sanya sunan dan wasan Crystal Palace na gefe Wilfried Zaha a tawagar 'yan wasan Ivory Coast da za ta je gasar cin kofin kasashen Afirka a Gabon.

An sanya dan wasan ne bayan ya yanke shawarar sauya kasar da yake yi wa wasa daga Ingila, inda ya girma, zuwa kasarsa ta haihuwa.

Shi dai Zaha mai shekara 24 an haife shi ne a Ivory Coast, amma ya buga wa Ingila wasa biyu, lokacin da ta yi da Sweden a watan Nuwamba na 2012 da kuma haduwarta da Scotland a 2013.

Saboda dukkanin wasannin biyu na sada zumunta ne, yana da damar ya koma yi wa kasarsa ta haihuwa wasa.

Kila dan wasan ba zai samu damar buga wa Palace wasannin mako shida ba, saboda gasar da zai je wadda za a fara a Gabon ranar 14 ga watan Janairu.

Shi ma dan Manchester United Eric Bailly ya samu gayyata a tawagar ta Ivory Coast mai 'yan wasa 24, daga kocin kasar, dan Faransa Michel Dussuyer.

Kocinya kuma gayyaci tsohon dan wasan kasar na gaba Salomon Kalou, wanda zai je gasar kofin Afirkan a karo na biyar.

Sai dai kocin yana kokawa da rashin Gervinho wanda yake jiyya, daga cikin 'yan wasan nasa, amma kuma ya ce zuwan Zaha, ya maye gurbinsa, domin kusan daya suke.

Zakarun na Afirka za su tafi Abu Dhabi inda za su fara atisaye daga ranar 2 ga watan Janairu.

Ivory Coast za ta fara gasar da Togo ranar 16 ga watan Janairu, kafin ta kara da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da kuma Morocco a wasan rukuni.