Oliseh ya zama kocin Fortuna Sittard ta Holland

Tsohon kocin Najeriya Sunday Oliseh

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Oliseh ya ajiye aikin kocin Najeriya bayan wata 10 kawai

Tsohon koci kuma kyaftin din Najeriya Sunday Oliseh, ya samu aikin horar da kungiyar Fortuna Sittard da ke rukuni na biyu a kasar Holland.

Oliseh, wanda ya ajiye aikin kocin Najeriya wata goma baya, ya yi wasa a kungiyar Ajax ta Holland din daga 1997 zuwa 1999.

Kungiyar ta Fortuna Sittard wadda ta tabbatar da nadin nasa a wata sanarwa ta shafinta na Intanet, ta ce ta kulla yarjejeniyar wata18 ne da Oliseh mai shekara 42, kuma yana da damar tsawaita kwantiragin da shekara daya.

Oliseh, wanda ya yi wasa a kungiyar Juventus da Borussia Dortmund ya buga wa Najeriya wasa sa 63.

Yan dan wasa ya dauki kofin kasashen Afirka da Najeriya a 1994 da kuma lambar zinare a gasar Olympic a 1996.

Kafin ya zama kocin Najeriya, ya yi aikin horar da wata 'yar karamar kungiyar ta Belgum, ta Verviétois.