'Shirin kara yawan kasashen kofin Duniya na samun karbuwa'

A gasar kofin duniya ta 1998, aka kara kasashe daga 24 zuwa 32

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Infantino ya yi kamfe da shirinsa na kara yawan kasashen gasar kofin duniya.

Hukumomin kwallon kafa na kasashen duniya sun bayar da gagarumin goyon baya ga shirin kara yawan kasashen gasar Kofin Duniya zuwa 48, in ji shugaban Fifa, Gianni Infantino.

A farkon watan nan ne shugaban na Fifa ya bayyana shirin nasa na fadada gasar ta kofin duniya, inda za ta kunshi rukuni 16 kowanne da kasashe uku-uku.

Bayan wasannin rukunin ne kuma kungiyoyin kasashen da suka zama na daya na biyu za su tafi zuwa zagaye na gaba na sili-daya-kwale.

A watan Janairu ne za a yanke shawara kan shirin, amma kuma ana ganin da wuya a sauya tsarin da ake da shi yanzu na kasashe 32, kafin gasar 2026.

Ranar tara ga watan Janairu ne majalisar zartarwar Fifa za ta tattauna kan shirin, wanda Infantino ya gabatar tun lokacin yakin neman zabensa.

A shekara ta 1998, aka kara yawan kasashen da ke shiga gasar ta kofin duniya daga 24 zuwa 32.

Hadakar kungiyoyin kwallon kafa na Turai, wadda ke jagorantar manyan kungiyoyin nahiyar ta yi watsi da shirin kara na fadada gasar ta kofin duniya.