Kocin Swansea: Giggs da Coleman na gaba-gaba

Luis van Gaal da Ryan Giggs a lokacin Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ryan Giggs ya yi wa Manchester United wasa 963 tsakanin 1990 da 2014

Swansea City na fatan nada sabon koci nan da Litinin, inda tsohon dan wasan Man United Ryan Giggs da kocin Wales Chris Coleman ke gaba-gaba cikin wadanda za a zaba.

A ranar Talata ne Swansea ta kori Bob Bradley bayan kwana 85 kawai da nada shi, yayin da kungiyar ke matsayi na 19 a teburin Premier.

Sau biyu shugabannin kungiyar na ganawa da Giggs, mai shekara 43, kafin nada Bradley a watan Oktoba.

Ba a san ko Giggs din zai yarda ya karbi aikin ba saboda abin da kungiyar ta yi masa a wancan lokacin, da ta bar shi ta dauki Bradely.

Tsohon kocin Leicester City Nigel Pearson da tsohon kocin Crystal Palace Alan Pardew da tsohon kocin Birmingham City Gary Rowett su ma suna cikin wadanda ke neman mukamin.

Ba a sa ran nada sabon kocin kafin wasan da kungiyar za ta yi na Premier a gida da Bournemouth a jajiberin sabuwar shekara.